Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana da masaniya a kan suaya fasalin wasu kuɗi da babban bankin Najeriya CBN zai yi.

A cewar shugaban kasa, Najeriya za ta amfana matuka da wannan yunƙuri da bankin ya yanke.
Ya kara da cewa ba ya tunanin watanni uku da aka baiwa mutane su canza kudin ya yi kadan.

Shugaban ya ce masu kudin haram da suka binne cikin kasa su ne suke tsoro, amma ma’aikata, yan kasuwa masu kudin halal ba zasu fuskanci wata matsala ba.

A jawabin da mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce Buhari ya bayyana hakan a hirar da yayi da ƴan jarida a fadarsa.
Shugaba Buhari a ranar Lahadi ya bayyana cewa shirin da babban bankin Najeriya CBN yayi na fitar sabon samfurin Naira ya na goyon bayan sa kuma kasar nan za ta amfana da hakan.