Kungiyar Arewa Consultative Forum reshen jihar Kano ta yi alkawarin kafa gidauniyar taimakon kudin makaranta ga ‘yan jihar da ba za su iya biyan kudin karatunsu na makarantun gaba da sakandare ba.

Sabon shugaban kungiyar, Dakta zura Faruk Gwani, ya bayyana hakan a Kano yayin jawabin amincewarsa inda yace wannan hukuncin ya zama dole saboda gwamnati na kasuwantar da fannin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, sabbin shugabannin an zabe su ne babu abokan hamayya a taron shekara-shekara da suka yi a Kano.

Sabon shugaban ya kara da cewa, kungiyar za ta nemi ‘yan takarar gwamnan daga jam’iyyun siyasa daban-daban don jin tanadinsu a kan ilimi, kiwon lafiya, tsaro, nima da karfafa matasa da mata.

Kamar yadda yace, sabbin shugabannin za su fifita fannin tsaro domin taimakawa hukumomin tsaro da kungiyoyin da kai wurin yaki da dukkan laifuka.

Yayin rantsar da sabbin shugabannin, shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar, Janar Halliru Akilu maj ritaya, yayi kira garesu da su tabbatar da amanar da aka basu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: