Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Gandujee ya gabatar da daftarin kasafin kuɗin shekarar 2023.

Gwamnan ya gabatar da kasagin a zauren majalisar dokokin jihar Kano a yau Juma’a.
Kasafin kuɗin da gwamnan ya gabatar ya kai naira biliyan 245 kuma daga ciki akwai kasafin da aka warewa ayyuka na musamman.

Haka kuma an ware naira biliyan 1.2 domin mata da masu buƙata ta musamman.

Wannan shi ne karo na ƙarshe da gwamnan zai gabatar da kasafin kuɗi yayin da wa’adin mulkinsa zai cika a shekarar 2023.