Gwamnatin jihar Kaduna ta ce an hallaka mutane 161  cikin watanni shida.

A daidai lokacin da rahotanni ke nuna cewar na yi garkuwa da mutane 1,789 a sassa daban-daban na jihar.

Hakka na ƙunshi a rahoton da Kwamishina tsaro da al’amuran cikin gida aya gabatarwa gwamnatin a ranar Juma’a.

Rahoton ya nuna cewar an kama mutane 654 da ake zargi da aikata ta’addanci da ya shafi garkuwa da mutane.

Sai dai gwamnan jihar Malam Nasiru El’rufa’i ya ce rashin tsaron da ake fuskanta a arewa maso yamma barazana ce ga zaɓen shekarar 2023 mai gabatowa.

Sai dai gwamnatin jihar za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin jami’an tsaro sun yi aikinsu don daƙile duk wani yunƙuri na ta’addanci a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: