Wata kotu da ke birnin tarayya Abuja ta bayar da izinin garkame wani Limamin wata coci a gidan gyaran hali bisa kamashi da laifin damfarar daya daga cikin masu zuwa cocin sa har kudi naira miliyan 55 da dubu 45.

Lauya mai shigar da kara Barrister C.S Ogada ya bayyana cewa faston mai shekara 55 wadda cocin nasa ta ke yankin Dawaki da ke Abuja ya amshe wa matar kudaden ne bayan sihiri da yayi mata.

C.S ya ce Limamin cocin ya bai wa matar mazauniyar yankin Gwarimpa kwayar barkono guda uku tare da umartarta da ta tauna da kuma wanke fuskar ta da ruwan roba harma da wani sashi na jikin ta.

Ogada ya kuma kara da cewa Limamin ya kuma sake bukatar matar da ta kawo masa kamfutoci guda shida na’urorin jin kida na cocin kujeru Takalma 20 riguna 20 sinkin jakunkuna harma da biya masa da kudin hotal wanda kudin ya kama naira miliyan 50 da dubu 645.

Kazalika Lauyan ya ce faston ya damfarin matar ne da zimmar yi mata magani.

Barrister Ogada ya kara da cewa bayan matar ta dawo hankalin ta ta nemi da ya mayar mata da kudinta inda yayi mata barazana.

Bayan gama karanta wa wanda ake zargi kunshin tuhumar da ake yi masa ya musamta hakan tare kuma da neman bukatar beli.

Alkalin Kotun Muhammad Sulayman Ola ya bayyana cewa laifin da foston ya aikata ya sabawa sashi 325 da 397 na kudin manyan laifuka.

Daga bisani kuma Alkalin ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Nuwanban shekarar 2022 domin ci gaba da shari’ar.

Alkalin ya ce kafin zuwan ranar ci gaba da shari’ar kotun za ta yi nazari tare da sanya masa sharadin belin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: