Gwamnatin jihar Kaduna ta jaddada kudirinta na baiwa kowane yaro da ke zaune a jihar ilimi kyauta tun daga matakin firamare har sakandare a bangaren fasaha da sana’a.

Gwamnatin ta bayyana cewa, takardar da tafito daga ma’aikatar ilimi zuwa ga shugabannin makarantu kan karbar kudaden makaranta, ta sabawa manufofin gwamnati.
Gwamna Nasir El-Rufai, ya bayar da umarnin soke takardar da ma’aikatar ilimi ta tura zuwa ga shugabannin makarantu, mai kwanan watan 1 ga Nuwamba, 2022, da gaggawa, sannan a mayar da duk wasu kudaden da aka karba daga hannun daliban makarantar nan take.

Gwamnan na Kaduna ya bayyana hakan ne a wani taro na majalisar zartarwa ta jihar Kaduna da aka gudanar a jihar, kuma gwamnan ya kara bayyana samar da ilimi kyauta na tsawon shekaru 12 na karatu a matsayin wani babban nasara da gwamnatin ta gada kuma za ta tabbatar da ita.

Wata sanarwa da mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa, Muyiwa Adekeye, ya sanyawa hannu a ranar Talata, ya ce gwamna El-Rufai ne da kansa ya jagoranci zaman majalisar zartarwa ta jihar, wacce ta haramta biyan kudaden PTA da sauran kudaden haraji a makarantun gwamnati.
Takardar ta tabbatar da cewa manufar ilimi kyauta a jihar, shine iyaye su hutu da biyan kuɗin makaranta da kananan haraji da makarantu ke karɓa a baya.