Babban Bankin Najeriya CBN, ya umurci dukkan bankunan dake Najeriya su fara bude kofofinsu daga ranar Asabar har zuwa ranar 31 ga Junairu don mutane su samu damar mayar da kudadensu.

Abaya mun kawo muku rahoton cewa ranar 15 ga Disamba, 2022, bankin CBN zai fitar da sabbin takardun Nairan N200, N500, da N1,00 .

Diraktan Yada Labaran Bankin, Osita Nwasinobi, ne ya sanar da wannan umurni da aka yiwa bankunan.

Ya bayyana hakan ne a wani taron baja kolin CBN da ya gudana ranar Alhamis a Ilori, birnin jihar Kwara.

Nwasinobi ya samu wakilcin mukaddashin Diraktan sadarwan bankin, Akpama Uket.

Ya ce an umurcesu su fara karban kudaden Naira koda nawa ne duk da hakan ya sabawa tsarin da aka shirya.

Biyayya ga umurnin CBN na tattara kudaden Naira dake yawo cikin jama’a, wasu bankuna sun sauya lokutan aikinsu don mutane su samu damar kai kudadensu.

A sakon akwatin email da suka aikawa kwastamominsu, bankunan sun bayyana cewa sun sauya ranakun aikinsu ne don taimakawa kwastomomi wajen zuba kudadensu a banki kan ranar 31 ga Junairu da CBN ya bada wa’adi.

Bankunan da aka ga sanarwarsu kawo yanzu sun hada da Ecobank, UBA da Access Bank.

[contact-form][contact-field label=”Name” type=”name” required=”true” /][contact-field label=”Email” type=”email” required=”true” /][contact-field label=”Website” type=”url” /][contact-field label=”Message” type=”textarea” /][/contact-form]

Leave a Reply

%d bloggers like this: