Ofishin Manejin basussukan Najeriya (DMO) ya bayyana cewa akwai bukatar gaggawa na gwamnatin tarayya ta rage karban basussuka don a iya biyan na kasa.

Dirakta Janar na ma’aikatar DMO, Patience Oniha, ta bayyana hakan ranar Alhamis a wani workshop da aka shiryawa yan majalisa.
Ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta nemo hanyar rage kashe kudi, samar da isassun kudin shiga sannan kuma a tabbatar bashin da za’a karba ayyuka za’a yi dasu wadanda ribar za’a samu da su zasu iya biyan bashin.

Tace yanzu basussukan gida da na waje sun yiwa Najeriya katutu kuma kudin ruwa na kara yawa.

A cewar ya kamata a rage karban bashi kuma a mayar da hankali kan samar da kudin shiga daga bangaren man fetur da sauransu.
Ta ce daga watan Yuni 2022 dai ana bin Najeriya bashin N42.8 trillion (N26.2 trillion na gida, N16.6 trillion na waje).