Rundunar yan sanadan jihar Kebbi ta tabbatar da kubutar da wasu mutane biyar da aka yi garkuwa da su a kwanakin baya  a jihar.

Kwamishinan yan sandan jihar Ahmad Magaji Kontagora shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a birnin Kebbi.

Ya ce cikin wadanda aka yi garkuwa da su akwai jamila Ahmad  shamsiya da Ahmad tasiu Haruna kuma an yi garkuwa da su a karamar hukumar wusagu.

Sannana ya ce an kubutar da mutane wadanda suka hada da mata biyu  da kuma wani namiji wanda aka yi garkuwa  da su a kusa da Bena akan babbar hanyar Mairairai amma yanzu haka sun kubuta.

Mutanen da aka kubutar da su an hada su da iyalansu.

Kantagora  ya ce sun samu sanarwar akan yan bandiga sun shiga yankin Bena Mairairai da jin haka suka tura jamiai cikin  gaggawa domin kai dauki.

Kuma ya ce sun yi garkuwa da  Aliyu Dankoji  hajiya hauwa biyu an yi garkuwa da su Rantsuwa  Makaranta karamar hokumar Suru mutane a yankin wanda bayan zuwan jami’an  su ka kubutar da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: