Babban bankin bayar da lamuni na duniya IMF ya bayyana cewa  Najeriya na kara fuskantar barazanar fadawa cikin matsalar karancin abinci a halin da ake ciki.

Cikin rahotanni da su ka fito daga bankin ya nuna cewa saboda hauhawar farashi da ambaliyar da aka fuskanta da kuma yakin da aka yi tsakanin kasahen Rasha da Ukraine wanda  hakan ya jawo tsadar kayan abinci hakan zai sa abinci yayi wahala.

Sannan idan aka yi duba da wannan yanayi da ake ciki abinci zai yi wuya a shekarar 2023 musamman a Najeriya.

Hukumar kididdiga ta kasa NBS ta ce hauhawar farashi a Najeriya ya kai kashi 23.72 cikin 100 a watan oktoban 2022 kuma ya karu zuwa kashi 50 cikin 100.

NBS ta ce yan kasa Najeriya miliyan 133 ke fama da talauci kuma galibinsu ba sa samun ilimi, tsaro da  kuma ishashiyar lafiya.

Kasa Najeriya kasa ce wadda ta shafe tsawon shekaru ta na fama da rashin tsaro matsalar ilimi tare da tsadar kayan abinci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: