Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana shakkunsa game da amfani da fasahar zamani wajen shirya babban zaben 2023.

Sanata Abdullahi Adamu ya nuna shakkunsa ne a lokacin da ya zauna da tawagar kungiyar da ke kula da kasashe rainon Burtaniya.
Adamu ya ce ya na ganin zai yi wahala wadannan nau’rori su iya aiki da kyau a lokacin da ‘yan Najeriya su ke fama da karancin wutan lantarki.

Hukumar INEC dai ta ce za ta yi amfani da na’urar BVA da IReV domin a tantace masu kada kuri’a kafin su yi zabe da kuma dora sakamakon zabe a yanar gizo.

Bayan haka Jama’a za su iya amfani da shafin IReV domin ganin sakamakon zaben shekarar 2023 kai tsaye, Kuma Sabuwar dokar zabe ta amince a yi amfani da na’urorin.