Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’anati ta EFCC ta bayyana cewa ta kwace kudade kimanin miliyan 755 a hannun tsohon akanta na kasa wato Ahmad Idiris.

Shugaban hukumar na kasa Abdurasheed bawa shi ne ya bayyana haka ga manema labarai yayin da ya bayyana nasarorin da EFCC ta samu cikin shekara Daya.
Sannan ya ci gaba da cewa sun kwace akalla kadarori 40 a hannun tsohon dan majalisar tarayya wato Ike Ekweremadu tsakanin kasashen Najeriya Ingila Amurka da kuma Dubai.

Bawa ya ce sun samu Nasara a Shari’o’i 3,328 wadanda aka yi su a fadin Najeriya.

Kuma sun kwace wasu makudan kadarorin daga hannun kanal Bello fadile, baya ga haka a makon da ya gabata kotu ta bayar da umarni akan karbe kadarori biyu daga hannun tsohowar minista Diezani Alison.
Abdurasheed bawa shi ne Wanda ya bayyana haka cikin nasarorin da EFCC ta samu cikin watanni 11 da farawarsa aiki a matsayin shugaba tun bayan zargin tsohon shugaban hakumar Ibrahim Magu da almundahana.