Gwamnan jihar Kano Dakta Abdulahi umar Ganduje ya amince da naɗa Dakta Zainab Ibrahim Braji a matsayin babbar darakta a hukumar kula da filaye ta jihar Kano.

Takardar mai ɗauke da sa hannun gwamna Ganduje ya siffanta ayyukan Dakta Zainab Braji a matsayin jajirtacciya wadda ke aiki da ƙarewa a ɓagarorin da ta riƙe.
A wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Malam Abba Anwar ya sanyawa hannu, sanarwar a ce gwamna Ganduje ya hori babbar daraktar da ta ruɓanya ƙoƙarinta don ganin an samar da sabuwar jihar Kano.

Sannan ya buƙaceta da ta yi amfani da fasahar zamani wajen tsarawa da kuma yin aiki kamar yadda ya santa a muƙaman da ta riƙe a baya.

Sanarwar ta ce gwamnan ya duba ƙarewar Dakta Braji tare da sanyata a matsayin babbar darakta domin samar da cigaba a jihar Kano.
Haka kuma ya buƙaceta da ta yi amfanio da ƙarewa a aikinta wajen yin gogayya da sauran birane na ƙasashen duniya.