Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa zata dawo da jigilar jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ranar biyar ga watan Disamba.
Manajan darakta na kamfanin jiragen kasa na Najeriya NRC, Fidet Okhiria ya bayyana hakkan ga kamfanin diillancin labaran Najeriya NAN.

Fidet ya ce dukkan shirye-shirye sun kammala domin dawo da sufurin jiragen.
Manajan daraktan ya shawarci fasinjojin da ke son yin tafiye-tafiye a jirgin da su fara sabunta manhajar wayoyinsu na hannu tun daga ranar 3 ga watan disamban da mu ke ciki.
Ya ce kamfanin zai fara jigilar ne da jirage biyu daga Abuja zuwa Kaduna da kuma Kaduna zuwa Abuja.

Kazalika shugaban ya kara da cewa jirgin AK 1 zai tashi daga tashar Idu da karfe 9’45 na safe ya isa tashar Rigasa da karfe 11’53 na safe, yayin da AK 2 zai tashi daga tashar Rigasa da karfe 8’00 na safe ya isa tashar Idu da karfe 10’17 na safe.

Shugaban ya tabbatarwa da fasinjoji cewa gwamnatin tarayya za ta tabbatar da tsaron rayukansu da dukiyoyinsu a kowanne lokaci.