Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnonin jihohin kasar na sa ce kason kudaden da ake turawa kananan hukumomi duk wata daga gwamnatin tarayya.

Shugaban na wannan zargi ne a taron manyan jami’an gwmnati na wannan shekara, na cibiyar nazarin manufofi da dabaru ta kasa [NIPSS] da ke birnin Jos na jihar Plateau.
Cibiyar na yin nazari ne duk shekara game

da wani mahimmin al’amarin da ya shafi kasa baki daya,

Kazalika cibiyar ta yi nazari akan haka kuma a karshe ta gabatar da sakamako da shawarwari, yayin da wannan shekarar cibiyar tayi nazari kan batun mulkin kananan
hukumomi, kamar yadda shugaban kasa ya bada umarn.
Mai magana da yawun shugaban kasa malam Garba Shehu wanda ya wakilci shugban a yayin taron ya shaidawa manaema labarai cewa cibiyar ta kammala aikinta na wannan shekara ta kuma bayar da
shawarwari kamar yadda ta saba, Shehu.
Shehu ya ce mahimmai da ga ciki sun hada da rashin tsari na dimuradiyya.
Shugaba Buhari ya ce yanzu haka jihohi 20 kawai suke da zababbun shugabannin kananan hukumomi da jama’a suka zaba
yayin da sauran ke gudanar da mulki karkashin tsarin kantomomi wanda ba zababbu bane.
cibiyar ta ce akwai rashawa da cin hanci a kasar, baya ga rashin fahimtar aiki, da kuma rashin kwarewa daga ma’aikata da kuma karancin kudade da za’a gudanar da ayyuka.