Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya bukaci kotu da ta soke hukuncin dauri da wata kotu ta yanke masa sakamakon kin biyayya da kotun ta ce yayi mata.

Akali Baba na neman soke hukuncin ne a gaban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja bayan da wata kotun ta bada umarnin daure shi har na tsawon wata uku sakamakon raina umarnin kotu na dawo da Patrick C. Koli bakin aikinsa na dan sanda, bayan an sallame shi ba bisa ka’ida ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya Olumuwiya Adejobi, ya ce tun kafin a nada Alkali Baba a matsayin shugaban ‘yan sanda magabacinsa ya dauki matakan doka don aiwatar da umarnin dawo da Patrick C. Koli bakin aikinsa.

Don haka shugaban ‘yan sandan ya bukaci kotun da ta soke hukuncin, domin ba shine ke kan kujerar ba a lokacin da aka ba da umarnin da kotun baya ta ce ya saba.
Bukatar da Sujeton ya shigar a ranar Alhamis ta bayyana cewa tun kafin umarnin kotun na watan Nuwamba na shekarar 2018, da na Janairu na shekarar 2019.

Magabacinsa ya aike wa hukumar kula da ayyukan ‘Yan sanda takardar neman ta baiwa Okoli takardar dawowa na shi bakin aiki da kuma kara masa girma zuwa matakin da ya da ce.
Adejobi ya ce don haka babu bukatar zaman kotun, Shugaban na bai wa ‘yan Najeriya aniyarsa na bin doka da oda, don haka babu yadda zai saba da umarnin kotu