Hukumar sadarwa ta kasa NCC ta ja kunnan al’umma kan siyan wasu wayoyi tare da yin amfani da su wanda hukumar bata yadda da ingancin su ba.

Hukumar ta bayyana hakan ne a lokacin da tawagar hukumar ta kama wani mai suna Yahya Ado na Gezawa Communications Limited kan zarginsa da sayar da wayoyi marasa kyau na kamfanin Gionee.
Hukumar ta ce bayan kama wanda ake zargi ya gaja wajen nuna shaidar fara sayar da wayoyi daga hukumar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa shugaba sashin aiwatar wa na kamfanin Malam Salis Abdu shine wanda ya jagoranci tagwagar.

Malam Abdu ya nuna rashin jindadin sa dangane da wayoyi marasa kyau da wadanda ba a amince da su ba su ka yawaita a kasuwar waya ta Beirut da ke Kano
Sanarwar da hukumar ta fitar ta yi gargadi cewa yin amfani da wayoyin da ba a amince da su ba ka iya haifar wa masu amfani da su asara.
Hukumar ta kuma zayyano a dadin wayoyi 1,891 daga kamfanoni ma banbanta wanda hukumar ta yarje yan Najeriya su yi amfani da su.
Daga cikin wayoyin da kamfanin ya amince da amfani da su sun hada Nokia Samsung Huawei LG Itel Sony da sauran su.
Hukumar ta NCC ta ce dukkan wanda aka kama da sayar da jabun wayoyin ga mutane za ta dauki tsatstsaran hukunci akan sa.