Hukumar shirya jarabawa ta kasa (NECO) ta ce za ta kawo karshen satar jarrabawarta ta hanyar tura jami’an hukumar tsaron farin kaya da kare dukiyar al’umma (NSCDC) zuwa cibiyoyinta.

Sannan hukumar ta ce za ta hada kai da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) domin shiga cikin lamarin.
jaridar Punch ta ruwaito cewa, Ibrahim Wushishi wanda yake a matsayin babban shugaban hukumar NECO, ya bayyana irin ci gaban da aka samu a wajen wani taron karawa juna sani da aka gudanar a garin Uyo na jihar Akwa Ibom.

Shugaban hukumar ta NECO ya yi kira da a

hada karfi da karfe domin magance matsalar tabarbarewar jarabawa.
Wushishi ya ce akwai bukatar a gaggauta dakile matsalar domin tabbatar da ci gaban kasa baki daya.