Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Ibrahim Gambari ya yi kira ga ma’aikatan gwamnati su yi koyi da Shugaba Buhari.

Gambari ya yi wannan kiran ne yayin jawabin da ya kaddamar a dakin taro da gyaran asibiti da Buhari ya yi a fadar gwamnati.
Farfesa Gambari ya yaba da salon shugabancin Buhari wanda ya ce ya kuduri aniyar barin Najeriya fiye da yadda ya tarar da ita.

Sannan Gambari ya shawarci manyan ma’aikata da suyi koyi da Shugaba Muhammadu Buhari wurin samar da ababen more rayuwa da karfafawa kananan ma’aikata gwiwa don yin ayyukansu.

Gambari ya bayyana hakan ne lokacin da ya kaddamar da cibiyar bada horaswa mai wurin zaman mutum 54 wacce aka kawata da na’urorin sadarwa na zamani da sabbin motoccin asibiti uku da gyara da aka yi a asibitin fadar shugaban kasa a ranar Alhamis, a Abuja.
Ya yaba da salon shugabancin shugaban kasar, yana mai cewa za a rika tunawa da shugaban kasar saboda ya bar tarihi na jogaranci a aikace da nagarta, Sanna Shugaba Buhari ya kuduri aniyar barin Najeriya fiye da yadda ya tarar da ita.a cewar shugaban ma’aikatan.
Yace idan kowa ya yi iya kokarinsa don inganta abin da ya tarar, a lokacin da shugaban kasa zai bar ofis a karshen wa’adinsa, zai bar abubuwa fiye da yadda ya tarar da su.
Yayin da ya ke yaba cigaba da aka samu a asibitin, Gambari ya ce gyara sashin asibitin da aka yi zai inganta ayyukan ma’aikata da sauran masu ziyartar asibitin.
Ya kuma jinjinawa Shugaba Buhari saboda ya karfafawa ma’aikatan fadar gwamnati da dukkan ma’aikatun gwamnati gwiwa su gudanar da aiki gwargwadon iyawarsu.
Gambari ya bayyana wata halayyar Shugaba Buhari da ba kowa ya sani ba
A wani rahoton, Ibrahim Gambari ya ce shugaba Muhammadu Buhari mutum ne da ke sakawa biyayya.