Hukumar da ke tabbatar da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta bayyana cewa nan bada jimawa ba za ta fara kamen ‘yan kasuwa masu sayar da man sauya launin fata wanda aka fi sani da bilicin.

Mukaddashiyar babbar darakta a hukumar dakta Monica Eimunjeze ce ta tabbatar da hakan a gurin taron karawa juna sani da hukumar ta shirya.

Dakta Monica ta ce hukukar za ta fara amfani da karfin ikon ta akan masu sayar da kaayan kwalliya da kuma masu hada mayukan da ba a yadda da su ba.

Monica ta bayyana cewa a wannan lokacin maza sun fi mata amfani da man na sauya launin fata .

Ta ce dukkan dan kasuwar da aka samu da sayar da man na sauya launin fata za a yi masa hukunci.

Monica ta ce Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke amfani da mayukan na sauya launin fata wanda hakan kuma illa ya ke haifarwa ga masu yin amfani da shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: