Fitacce kuma babban Lauya mai kare hakkin Bil Adama, Femi Falana ya soki sabon tsarin babban bankin kasa CBN na takaita cire kudi a Najeriya.

A wani jawabi da ya fitar a ranar Litinin, Femi Falana yace tsarin ya sabawa ka’ida, don haka ba zai yiwu ya yi aiki ba.

Lauyan ya kara da cewa tsarin ya ci karo da sashe na 2 na dokar hana safarar kudi ta shekarar 2022, yace naira miiyan biyar ne abin da doka ta haramta yawo da shi.

Masanin shari’ar yace ba ayi wa wannan doka kwaskwarima ba, don haka babu yadda Gwaman CBN zai takaita cire kudi zuwa N100, 000 a mako.

Falana ya yi kira ga al’ummar Najeriya suyi watsi da wannan sanarwa da ya ce ta saba doka.

An ruwaito Lauyan ya na kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci shugabannin bankin CBN su janye wannan tsari da zai kawo kunci ga mutanen kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: