Tsohon Sarkin Kano Muhammad Sanusi II wanda ya rike babban bankin Najeriya tsakanin shekarar 2009 zuwa 2014, ya goyi bayan sabon tsarin rage amfani da kudin takarda.

A wani jawabi da yayi bayan karatun da ya saba yi, tsohon Sarkin Kano ya fadawa jama’a cewa tsarin da za a fito da shi zai fi yin maganin ‘yan siyasa ne.

Muhammad Sanusi II ya zargi ‘yan siyasa da zaluntar talakawa na tsawon shekaru, idan lokaci zabe ya karaso, sai suyi amfani da kudi domin suyi nasara.

Basaraken ya ce tsarin da aka fito da shi zai jawo rike kudi ya yi wa ‘yan siyasa wahala, a dalilin haka sai a samu karancin kudin da za ayi magudi.

Ya ce bata-garin ‘yan siyasan Najeriya sun saba amfani da dukiya wajen sayen ‘yan daba, jami’an tsaro, malaman zabe domin komawa kujerunsu.

A rahoton da manema labarai suka kawo an ji masanin tattalin arzikin yana cewa wannan tsari da CBN ya fito da shi shi zai fara rage barnar da ake yi wajen tafka magudin zabe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: