‘Yan majalisar dattawan Najeriya sun nemi shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya dakatar da aikin wutar Zungeru,

kwamitin majalisar kan harkar makamashi shi ne ya yi kiran bayan dogon nazari a kan yadda aikin ke gudana.

Shugaban kwamitin, Sanata Gabriel Suswan, a yayin zaman kwamitin ya ce ba wai ba a bukatar gudanar da aikin ba ne, sai dai tafiyar hawainiyar da aikin ke yi ne ta sa suka yanke wannan hukunci.

Ya ce, baya ga tafiyar hawainiyar da aikin ke yi babu kuma wadatattun kayan aikin da ake bukata.

Sanata Suswan, ya ce a don haka suka bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da aikin har sai an samar da kayayyakin da ake bukata wajen gudanar da aikin samar da wutar lantarkin a Zungeru.

Kididdiga ta nuna cewa a tsakanin shekarar 2015 zuwa shekarar  2022 da muke ciki, babban layin da ke ba wa Najeriya wuta sau 98 ya na samun matsala, abin da ke jefa mutane da dama cikin duhu da kuma durkusar da harkokin kasuwanci a wasu sassan kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: