Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce magance matsalolin da suka addabi matasa ne abin da gwamnatinsa ta sa gaba, domin cika alkawarinsa na samar da kyakkyawar makoma ga matasan Najeriya.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne lokacin da babban sakataren zauren samar da zaman lafiya Abu Dhabi, Sheikh Al-Mahfoudh Bin Bayyah da takwaransa na Amurka Fasto Bob Roberts suka kai masa ziyara a ranar Talata a birnin Washington DC da ke kasar Amurka.
Buhari ya ce aikin da gidauniyar ke yi na inganta tattaunawa tsakanin addinai na da matukar muhimmanci ga duniya da ma Najeriya.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya fitar, ya ce akwai bukatar samar wa matasa yanayi mai kyau don guje musu fadawa cikin ayyukan masu tsattsauran ra’ayi, sannan kuma ya bukaci kungiyar da ta ci gaba da kai dauki kan matasa don su ne manyan gobe.

Sakataren ya ce sun kai ziyarar ne don gayyata tare da karrama shugaba Buhari da gidauniyar ta shirya kan nasarorin da ya samu wajen inganta zaman lafiya da tsaro.
Ya kara da cewa karramawar wani sashe ne na aikin gidauniyar na yaki da tsattsauran ra’ayi da kuma samar da zaman lafiya a tsakanin addinai.