Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa ta NEMA ta tabbatar da dawo da ‘yan Najeriya su kimanin 105 daga kasar Chadi.

Babban jami’i mai lura da harkokin shingaye na hukumar a nan Kano, Dr Nuraddeen Abdullahi, shi ne ya bayyana hakan ga manema labara yayin karbar mutanen da aka yi nasarar dawo da su.

Ya ce mutanen da suka dawo sun sauka ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da misalign karfe goma na daren jiya Talata.

Dr Nuraddeen ya kara da cewaan samu nasarar dawo da mutanen zuwa nan gida Kano bisa kulawar kungiyar lura da ‘yan gudun hijira ta duniya karkashin shirinsu na dawo da baki kashensu na asali.

Har ila yau ya bayyana cewa ya bayyana cewa za a bawa mutanen da aka dawo da su wani horo na kwanaki hudu akan koyar da dabarun kasuwanci da kananan sana’o’i domin dogaro da kansu. Inda ya ce shirin zai sake wayar da kansu na daina yin kaura zuwa wasu kashen duniya ba bisa kaida ba.

Tsakanin watan Mayu zuwa watan Oktoban wannan shekara ta 2022, hukumar ta NEMA ta karbi kimanin ‘yan Najeriya 560 wadanda suka yo kaura daga kasashen Nijar da Sudan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: