Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta ce jami’anta sun kashe wasu ’yan bindiga da suka addabi kauyuka da garuruwan jihar Katsina.

Rundunar ta ce an kasha ‘yan bindigar ne kafin wayewar garin ranar Laraba, a lokacin da ’yan ta’addan suka kai hari cikin dare a Karamar Hukumar Dutsinma ta jihar.

Kakakin rundunar yan sandan jihar ta Katsina SP Gambo Isah ya ce kasurguman ’yan bindigar biyu da aka kashe su ne Abu Na-Iraqi da Abu Na-Masari.

Ya ce an kashe su ne lokacin da suka kai hari yankin Sokoto Rima da ke Karamar Hukumar Dutsinma a jihar.

A daren jiya Talata ne dai misalin karfe 7:30 na dare ’yan bindiga dauke da bindigogi kirar AK-47 suka kai hari yankin Sokoto Rima da ke Karamar Hukumar Dutsinma da nufin sace mazauna yankin.

Sai dai kwamandan ’yan sandan yankin da dakarunsa sun kai dauki, inda suka yi artabu da ’yan bindigar har suka yi nasarar kashe ’yan bindigar da aka dade ana nema.

SP Gambo Ya ce an kashe ‘yan bindigar ne lokacin da suka kai harin, sannan ya kara da cewa an kwato bindiga kirar AK-47 guda biyu da makamai masu yawa daga hannun miyagun.

Haka-zalika ana ci gaba da gudanar da bincike a yankin da kewayensa don cafke sauran ’yan bindigar da suka tsere da raunin harbi a jikinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: