Shugaban jam’iyyar APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu, ya bugi kirjin cewa Tinubu ne zai karbi Buhari, shugaban jam’iyyar ya yi wannan ikirari ne a lokacin gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na yankin Arewa maso Yamma, inda ya ce yadda mutane suka yi cikar kwari a wajen ya tabbatar da irin farin jinin Jam’iyyar APC a wurin ’yan Najeriya.

Abdullahi Adamu ya kuma yaba wa magoya bayan Jam’iyyar APC daga jihohin Kano, Katsina, Sakkwato, Kebbi, Zamfara da Jigawa da suka yi dafifi wajen halartar taron a jihar Kaduna.

Tunda farko Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa yawan jama’ar da ta taru a taron yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na APC ya zama izina ga sauran jam’iyyu.

Tun gabanin taron, a ranar Litinin, Tinubu ya je Birnin Gwari, yankin da ’yan bindiga suka kafa wa kahon zuka a Jihar Kaduna, inda ya jajanta wa al’ummar yankin, tare da ba wa wadanda hare-haren ’yan bindiga suka shafa tallafin Naira miliyan 50.

Ya kuma yi alkawarin gina madatsan ruwa na zamani domin magance matsalar karancin ruwa da suke fama da ita a yankin idan ya ci zabe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: