Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya sanar da bayar da tallafin biliyoyin daloli don ciyar da Afirka gaba a yayin taron shugabanin kasashen Afirka da ke gudana a Washington na kasar Amurka.

Amurka za ta zage dantse kan ci gaban Afirka, a cewar shugaba Biden da yake sanar da shugabannin kasashen Afirka 40 da suka halarci taron.

Haka kuma ya bayyana aniyar Amurka ta ci gaba da karfafa dangantakarta da Afirka, inda ya sanar da bai wa kasashen tallafin dala biliyan 55 a matsayin sabon tallafi ga Nahiyar na tsawon shekaru uku ciki har da dala miliyan 100 na samar da makamashi.

Ya sanar da mahalarta taron cewar idan Afirka ta yi nasara, haka ma Amurka zata zame mata babbar nasara duba da irin kyakkyawar alakar dake tsakanin Amurka da kasashe nahiyar Afirka.

Mr Biden ya yi jawabi kan muhimmancin shugabanci na gari, samar da jama’a mai koshin lafiya da makamashi mai sauki.

Ana kallon taron shugabanin kasahen Afirka da ke gudana a Amurka a matsayin wani yunkuri ne da kasar ta Amurka ke yi na ganin ta dawo da karfin ikon ta kan nahiyar a daidai lokacin da kasashen China, Rasha da Turkiya ke fadada damarsu a nahiyar.

Wannan ne dai karo na farko a shekaru takwas da kasar Amurka ta karbi bakunci irin wannan taro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: