Gwamnatin Tarayya ta bayyana damuwarta kan yadda mutane ke fargabar fallasa barayin da ke yin awon gaba da dukiyar talakawa.

An dai kirkiro shirin ne a shekarar 2016, inda gwamnati ta amince a bai wa kowane mutum da ya gabatar da irin wadannan bayanai kuma aka gano kudaden tsakanin kashi biyu da rabi zuwa kashi biyar na kudin da aka kwato.

Ministar Kudi, Zainab Ahmed, ta ce gwamnati ta yi nazarin gabatar da wannan tsari ne a karkashin shirinta na yaki da cin hanci da rashawa, abin da ya kai ga kafa wani kwamitin da yake dauke da wakilan gwamnati da kuma na hukumomin yaki da cin hanci irin su EFCC da ICPC da hukumar tsaron DSS da kuma sashen rundunar ‘yansandan da ke yaki da almundahana wato  NFIU.

Zainab, ta ce ganin yadda aka samu koma baya wajen samun bayanai ya sa gwamnati ta kaddamar da taruka a shiyyoyin kasar nan, abin da ya nuna mata cewar mutane na fargaba wajen gabatar da bayanan irin wadanann mutane da ke satar kudaden talakawa.

Bayan kaddamar da shirin, gwamnatin tarayya ta yi nasarar kwato biliyoyin kudade a hannun jami’an gwamnati abin da ya kai ga daure wasu daga cikin wadanda aka samu da laifi.

Yayin da wasu daga cikin mutanen da suka gabatar da bayanan satar suka samu tukuicin da aka musu alkawari, wasu sun gabatar da korafin cewar an hana su kudaden da aka musu alkawari, yayin da bayanan da suka gabatar suka jefa rayuwarsu cikin hadari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: