Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya bayyana cewa hukuncin da aka yanke wa Darakta-Janar na yakin neman zabensa, Doyin Okupe, kan badakalar kudade ba zai karya kudurinsa na zama shugaban Nijeriya a 2023 ba.

Obi ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya (NUJ), a Uyo, sakatariyar kungiyar da ke Jihar Akwa Ibom a ranar Litinin.

Tsohon gwamnan na Jihar Anambra, ya ce hukuncin bai taka kara ya karya ba, kuma zai ba da damar bin doka da oda don gudanar da aikinsa.

Abaya an rawaito cewa an samu Okupe da laifi 26 cikin 59 da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC), ke tuhumarsa.

Mai shari’a Ijeoma Ojukwu ta bayar da umarnin a gudanar da tuhume-tuhume 26, wadanda suka janyo masa zaman gidan yari na tsawon shekaru biyu kowane.

Leave a Reply

%d bloggers like this: