Wasu miyagu da ake zargin ‘yan bindiga ɓe sun yi awon gaba da ɗaliban kwalejin fasa hudu yayin da suke kan hanyar zuwa gida don halartar bikin al’ada a jihar Ondo.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an sace ɗaliban ne akalla su huɗu a kan Titin Akunno zuwa Ajuwa da ke yankin Akoko, a jihar Ondo, kudu maso yammacin Najeriya.

 

Gwamna Nasir Ahmed El-Rufa’i na Jihar Kaduna ya gabatar da sandan sarauta ga Alhaji Abdullahi Daniya a matsayin sarkin Jere na 11.

An yi bikin ne a filin wasanni na Jere a ranar Juma’a tare da matakan tsaro, Daily Trust ta rahoto.

 

Korarren dan takarar gwamna na PDP a jihar Kano, Sadiq Aminu Wali, ya bayyana niyarsa na zuwa kotun daukaka kara bayan babban kotun tarayya ta soke zabensa da aka yi a matsayin dan takarar gwamna a jihar.

Daily Trust ta rahoto cewa Babban Kotun Tarayya da ke Kano ta ayyana Mohammed Sani Abacha a matsayin halastaccen dan takarar gwamna na PDP a Kano.

 

Jami’an tsaro a Nijeriya sun kashe ‘yan fashin daji takwas tare da ƙwace babura yayin wani samame da suka kai a yankin Chikun da Birnin Gwari na Jihar Kaduna, a cewar gwamnatin jihar.

BBC ta rawaito cewa, Kwamashinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Kaduna Samuel Aruwan ya ce dakarun rundunar rundunar haɗin gwiwa na Operation Forest Sanity ne suka ƙaddamar wa ‘yan bindigar cikin sanarwar da ya fitar ranar Juma’a.

 

Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a Sakatariyar Audu Bako, ta dakatar da Gwamnatin Jihar Kano daga yunkurin da take yi na gina shaguna a jikin Makarantar Sakandiren Kwakwachi da ke Jihar.

Kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a Yusuf Ubale Muhammad, ta bayar da umarnin ne ranar Jumu’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: