‘Yan ta’adda sun hallaka Usman Garba dagacin kauyen Mulu dake karamar hukumar Mashegu a jihar Neja, bayan sunyi garkuwa da shi.

Kwamishinan tsaron cikin gida Emmanuel Umar ne ya bayyanawa manema labarai hakan jiya Juma’a a babban Birnin jihar na Minna.
Ya bayyana cewa, ‘yan bindigar sun mamayi kauyen Na Mulo a ranar Alhamis, yayin da suka yi garkuwa da dagacin kauyen da kuma wasu mutane guda hud’u.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, an hallaka dagacin ne biyo bayan yin garkuwa da shi. Kuma an jefar da gawarsa ‘yar tazara Kadan da barin garin. Sannan ‘yan bindigar suka tsere da sauran mutane hud’un da suka yi garkuwa da su.

A lokacin da yake tabbatar da faruwar lamarin kwamishinan ya bayyana cewa, duk da samun ingantuwar sha’anin tsaro a jihar. Har yanzu ana samun wasu hare-haren musamman a kananan hukumomin Mashegu, Mariga da kuma Kontagora.
Ya kuma bayyana cewa, an umarci jami’an tsaro a jihar da su binciko ‘yan ta’addar, kuma su kawo karshen matsalolin tsaro a yankin.