A kokarinta na tabbatar da ingantaccen tsarin ciyar daliban makarantun firamare, hukumar kyautata ci gaban al’umma (CPC) ta kammala shirye-shiryen ci gaba da samar da abinci mai gina jiki ga daliban faramare.

Shugaban hukumar, Honarabul Hafizu Sani Maidaji ya bayyana haka a lokacin gudanar da taron tattaunawa da masu harkokin ciyarwar, wanda ya gudanar a dakin taro na hukumar.

Hafizu Sani ya ce wannan ci gaba an tsara shi ne domin samar da kyakkyawan tsari kasancewar shekara ta 2022 na gaf da karewa, sannan kuma an samu hauhawar farashin abubuwan da ake bukata na shirin ciyarwar.

Shugaban ya bukaci masu aikin ciyarwar da su daina jinkiri wajen raba kayan abinci ga masu aikin dafawa.

Ya kuma tabbatar masu da cewa hukumar za ta ci gaba da sa ido kan shirin, domin tabbatar da ganin ana aiwatar da shi yadda ya kamata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: