Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El’Rufa’i ya yiwa mazauna gidan gyaran hali 11 afuwa wanda aka yanke musu hukunci daban-daban a Jihar.

El’Rufa’i ya yiwa fursunonin afuwar sakamakon murnar shigowar sabuwar shekarar 2023 da ta kama jiya.

An sallami mutanen ne kar kashin sashi na 212 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 da aka yiwa kwaskwarima.

Gwamna El’Rufa’i yayi afuwar ne karkashin kwamitin jin kai na Jihar wanda aka sallame su a ranar Lahadi daya ga watan sabuwar shekarar 2023.

A yayin bikin sabuwar shekarar da kungiyar KCTA ta shiyar gwamna yayiwa al’ummar Jihar bankwana sakamakon karewar wa’adin mulkin sa.

Kwamitin ya ce wadanda aka yankewa hukuncin shekaru uku ko watanni shida ko fiye da haka aka yafewa.

Daga cikin wadanda aka yiwa afuwa sun hada Yakubu Abdullahi Musa John Habu Usman Shamsu Usman Abdullahi Abdulmumin.

Sauran sun hada da Mahadi Abdullahi Future Mabuke Abdullahi Lawal Sunday Iliya Muhammad Anas da kuma Kayode Gabriel Adenji.

Leave a Reply

%d bloggers like this: