Akalla mutame bakwai ne su ka rasa rayukan su yayin da 16 su ka samu raunika a wani hadarin mota da ya afku a kan hanyar ibadan-Legas.

Kwamandan kiyaye afkuwar hadurra FRSC na Jihar Ogun Ahmad Umar ne ya bayyana faruwal lamarin ga manema labarai.
Hadarin ya faru ne a ranar Lahadin a lokacin da mutanen su ke tsaka da bukukuwan sabuwar shekara.

Kwamandan ya ce hadarin ya rutsa ne da motar Bas kirar Toyoto Hiace tare da tamkar mai.

Umar ya kara da cewa lamarin y faru da misalin karfe 4:10 na yammaci sakamakon gudun wuce sa’a da direban motar kirar bas ya ke yi.
Ahmad Umar ya ce gudun wuce sa’a da direban ya ke yi ne ya sanya ya daki motar dakon man ta baya.
Kazalika kwamandan ya ce mutane 25 a cikin motar da su ka hada da maza da mata ,inda su ka mika wadanda lamarin ya rutsa da su Asibiti domin kula da lafiyar su.