An sha fama da ambaliyar ruwa, yawan mace-mace, yajin aikin malaman jami’oi na tsawon wata takwas, satar mutane dan kudin fansa, tabarbarewar tattalin arziki na cikin abubuwan da sukaiwa shekarar 2022 katutu a NIgeria.

Hukumar kididdiga ta kasa NBS, ta ce a shekarar 2022 akwai ‘yan Nigeria kimanin Miliyan 133 da suke cikin kangin talauci baya ga yara kusan Miliyan 20 da basa zuwa makaranta, wanda hakan ke nuna fiye da rabin yan Nigeria matalauta ne kuma yaransu basu da ilimi.


Baya ga halin kunci da tatttalin arzikin kasar nan ya shiga, ‘yan siyasa sun fitar da wukakensu da ga kufe muraran da kuma neman darewa ko maimaita kujerunsu ko na sama da su a babban zaben da ke tunkarar kasar nan na shekarar 2023.
Abinda yake a bayyane shine mutane kusan 8,058 da doriya ne aka kashe a Nigeria sanadiyar tashe-tashen hankula dabam-dabam wanda suka hada da garkuwa da mutane, aikin ‘yan kungiyar Boko-Haram, aikin ‘yan awaren IPOB da dai sauransu.
Baya ga wadancan rashe-rashen da aka samu ta sanadiyar aiyukan masu kawowa kasar nan barazanar zaman lafiya, hatta hukumomin tsaron kasar nan sunyi sanadiyar rasa rayukan wasu daga cikin fareren hula a kasar sabida aiyukan na sakaci ko kuskure.