Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, yayi wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo tatas bayan ya soki Buhari.

A sakonsa na murnar shiga sabuwar shekara a ranar Lahadi, Obasanjo ya soki gwamnati mai ci karkashin shugabancin Buhari.


Yayin martani ga sukar da yayi a wata takarda da ya fitar ranar Litinin, Shehu ya ce Obasanjo na bakin ciki saboda Buhari ya sha gaban Obasanjo a bangaren kawo cigaban kasa.
Haka zalika, Shehu ya ce Obasanjo bashi da bakin sukar mulkin Buhari, inda ya kara da cewa tsohon shugaban kasar “ya lalata asalin dimokaradiyyar” sannan “yayi amfani da mulki a inda bai dace ba” a kan wadanda yake ganin makiyansa ne.
“Daya daga ciki shi ne, ba zai daina sukar shugaba Muhammadu Buhari ba saboda tsohon shugaban kasar ba zai daina hassada da duk wanda ya tsere masa ba a tarihin cigaban kasa.”