Hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta watau INEC, ta yi alkawarin cafke duk wasu ‘yan kasa da shekara 18 da aka kama za su yi zabe.

 

Kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a na hukumar INEC, Festus Okoye ya yi wannan bayani ne a wata hira da ya yi a gidan talabijin Arise.

 

Festus Okoye ya ce ana kokarin magance matsalar da ake samu ta ‘yan kananan yara su je su kada kuri’a, alhali sai ‘dan shekara 18 ne zai iya yin zabe.

 

Kwamishinan yake cewa a yunkurin ganin an tsabtace tsarin zabe, INEC ta taso duka jami’anta da aka samu ‘yan kananan yara sun yi rajista a wurinsu.

 

Za su bayyana a gaban wani kwamitin hukumar na musamman, kuma yanzu haka ana aikin.

 

Hukumar ta bakin kwamishinan, ta ce ana ta kokarin cire yara daga cikin rajistan zaben, kuma a karshe ‘Yan Najeriya za su ji dadin aikin da aka yi.

 

The Cable ta rahoto Okoye ya yi magana a kan kananan yaran da ake ganin hotonsu a rajistar INEC, ya ce wasu hotunan tun na zabukan 2011 ne.

Leave a Reply

%d bloggers like this: