Rundunar yan sandan jihar Katsina ta bayyana kashe Dan ta’addan ne a jiya Litinin, a wata musayar wuta da suka yi a wani shingen binciken ababan hawa Na karamar Hukumar Jibia a jihar ta Katsina.

Rundunar ta bayyana cewa Wanda ake zargin Ibrahim Dangawo, shugaba ne na yan ta’adda da suke yankin jihohin Katsina da Zamfara.
Ta kuma kara da cewa gungun yan kungiyarsa ta ta’addanci, sune suka kashe tsohon jami’in hukumar yan sanda na Jibia. Wato DSP Abdulkadir Rano a shekarar da ta gabata.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, mai magana da yawun rundunar yan sandan ta jihar Katsina SP Gambo Isah. Shine ya tabbatar da faruwar lamarin.

A Jiya Litinin ne dai gungun yan ta’addan suka kai hari a shingen binciken ababan hawa na yan sandan a mahadar Magama da Hirji, dake kan titin Katsina zuwa Jibia.
Yan sanda guda biyu ne dai suka samu raunuka yayin afkuwar lamarin, inda tuni aka basu magani kuma aka sallame su daga Asibiti.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan ta jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar da cewa, a daidai karfe Hudu da Rabi na cikin Dare.