Wasu mahara a Jihar Imo sun bankawa babban ofishin ‘yan sanda da ke yankin Atta a karamar hukumar Njaba ta Jihar.

Aika-aikar ta maharan na zuwa ne a wannan kadan bayan da wasu ‘yan bindiga su ka kaiwa tawagar tsohon gwamnan Jihar hari.

Bayan shigar ‘yan bindigar ofishin su ka dinga jefa wasu abubuwan fashe har ta kai ga sun tashi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa a yayin da ‘yan bindigan su ka kai harin babu wani jami’in dan sanda da ya ke bakin aiki.

Wata majiya daga Jihar ta bayyana cewa maharan sun je ofishin ne a daren ranar Litinin inda su ka kone shi kurmus.

Magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Micheal Abattam bai ce komai ba dangane da faruwal lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: