Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya ta cafke wasu mutane uku da ake zargin su da cin zarafin ubargidan shugaban kasa wato Aisha Buhari.

Daga cikin wadanda jami’an su ka kama sun hada da Isyaku Salisu Habib da kuma Zubairu Ahmad.

Wata majiya ta bayyana cewa kawo yanzu mutanen sun kashe tsawon makonni biyu a hannun jami’an ba tare da sake jim duriyar su ba.

Majiyar ta kara da cewa jami’an sun kama mutanen ne tun a ranar 14 ga watan Disambar shekarar 2022 da ta gabata.

Wajiyar ta ce an tafi da su ne zuwa Abuja inda har kawo yanzu babu Lauya ko wani dan uwansu da ya gana da su.

Kawo yanzu mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta kasa CSP Olumuyiwa Adejobi bai ce komai ba dangane da hakan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: