Wani kwamiti a karamar hukumar Tudun Wada a nan jihar Kano, ya bayyana cewa ya gano asibitoci da shagunan sayar da magunguna 130 da likitocin bogi ke tafiyar da su.

Kwamitin wadda shugaban karamar hukumar, Alhaji Tijjani Matata, ya kafa ya ce yayin bincikensa ya gano daya cikin likitocin injiniya ne na lantarki wanda ke da asibiti mai gado takwas da ya yi ikirarin yana maganin kowanne ciwo.
Shugaban kwamitin, Alhaji Abubakar Karafe ya fada wa manema labarai cewa daya daga cikin likitocin bogin ya saka wa wata mata jini mai cutar kanjamau lokacin da ta zo yin maganin zazabin cizon sauro.

Karafe ya ce abin takaici ne yadda mu ka gano injiniya na lantarki yana tafiyar da asibiti mai zaman kansa yana ganin marasa lafiya yana rubuta magani, yana karin ruwa, jini, har yana kulawa da masu ciki, Daya daga cikinsu ya saka wa wata mata mai ciki HIV.

Alhaji Tijjani ya ci gaba da cewa Mun gano wani mai maganin gargajiya, amma yana kwantar da masu kwalera,mun kwashe su mun kai su asibiti,inda mafi yawancin su ba su san komai game da kiwon lafiya ba.
Karafe ya kara da cewa daya daga cikinsu ya ce shi malamin jinya ne amma muka gano satifiket din kauyukansu.