Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana cewa ta kafa wani kwamiti da zai yi aikin tattarawa hukumar sakamakon shugaban kasa daga kowacce Jiha.

An kafa kwamitin ne karkashin jagorancin shugaban hukumar na kasa Muhammad Yakub.
Hukumar ta bayyana cewa zauren taro na cibiyar Taro ta kasa da kasa ICC da ke birnin tarayya Abuja ce za ta gudanar da aikin tattara sakamakon zaben shekarar da muke ciki.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a na hukumar Festos Okoye ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Okoye ya ce daga ranar Juma’a hukumar za ta fara karbar katunan zabe na dindindin daga Ofisoshin ta da ke mazabu 8,809 na fadin Kasa baki daya ga wadanda ba su karba ba.
Hukumar ta kuma sanya ranar 12 ga watan Disamba shekarar 2022 da ta gabata zuwa ranar 22 ga watan Janairun shekarar 2023 da mu ke ciki a matsayin ranakun karbar katunan zabe na dindindin.
Kazalika Okoye ya ce dukkan wanda katin sa ya fata koya lalace ko bai karba ba tun a shekarar 2019 su tafi izuwa ofisoshin hukumar na mazabu domin su karba.