Jami’an Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi sun kama wata mata mai suna Amina Guguwa mai shekaru 50 a duniya da ake zargin ta da hallaka kishiyar ta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Ahmad Wakil ya tabbatar da hakan ta cikin wata wasika da ya aikewa manema labarai a ranar Juma’a.

Wakil ya ce matar mazauniyar Kauyen Miya ce da ke karamar hukumar Warji ta Jihar.

Kakakin ya bayyana cewa Guguwa ta hallaka kishiyar ta tace mai suna Amina Koli mai shekaru 60 tun a ranar 1 gawatan Janairu 2023 bayan fada ya kaure a tsakanin su har ta kai ga tashake ta.

Ahmad Wakil ya kara da cewa bayan faruwal lamarin aka aike da Amina Koli Asibiti inda jami’an lafiya su ka tabbatar da mutuwar ta.

Wakil ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da ita agaban kotu domin yanke mata hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: