Shugaban kasa Muhammad Buhari ya mika sakon ta’aziyyar sa ga gwamnatin Jihar Kebbi da al’ummar Jihar baki daya sakamakon rasa rayukan mutanen Jihar da hadarin jirgin ruwa ya kife da su.

Mai magana da yawun shugaba Buhari na Musamman Femi Adesina ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

Shugaba Buhari ya jajantawa ‘yan uwa da iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su.

Buhari ya yi addu’ar samun sauki ga wadanda aka ceto su a yayin hadarin.

Shugaban ya jinjinawa ma’aikatan da su ka gudanar da aikin ceto mutanen da hadarin ya rutsa da su.

Shugaba Buhari ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki da su maida hankali akan tafiyar da jiragen ruwan yadda ya kamata musamman a bangaren karkara.

Buhari yayi addu’a da neman samun rahmar ubangiji ga wadanda su ka rasa rayukan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: