Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya ki amincewa da bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari na amfani da filin taro na Ribadu Square da ke jihar don kaddamar da kamfen APC a jihar.

Wannan na fitowa ne daga cikin wata takardar da gwamnan ya aikewa Buhari tare da sa hannun sakataren gidan gwamnati, Bashiru Ahmad, kamar yadda Legit.mg ta samo.
Wasikar ta bayyana dalilai da suka sa gwamnatin Adamawa ba za ta samu damar ba da filin taron ba, inda tace ana kan wannan babban aikin gyara a cikinsa.

Idan baku manta ba, ‘yar takarar gwamnan APC a jihar, Aisha Dahiru Ahmed (Binani) ce ‘yar takawar gwamna mace a manyan jam’iyyun siyasa na Najeriya guda biyu.

Ta tsaya takara ne domin kalubalantar Fintiri a zaben 2023 mai zuwa, wanda shi kuma gwamnan PDP ne kuma jigonta a jihar da ke Arewa maso Gabas.
Shugaban kasa Muhammadu, a bangare guda, zai halarci taron gangamin na APC a jihar Adamawa a ranar Litinin mai zuwa, amma wasikar ta zo ba yadda ake so ba daga gwamnatin Adamawa.