Rundunar ‘yan sandan Jihar ta samu nasarar ceto mutane 15 da wasu mahara su ka yi garkuwa da su akan hanyar Gusau zuwa Funtua.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Muhammad Shehu ne ya bayyana hakan inda ya ce jami’an sun samu nasarar ne bayan samun labaran garkuwa da mutanen.
Kakakin ya kara da cewa bayan samu rahotan garkuwa da mutanen su ka aike da jami’an zuwa cikin dajin .

Shehu ya ce jami’annasu sun yi musayar wuta da ‘yan bindigan wanda hakan ya sanya su ka tsere su ka bar mutanen.

Muhammad Shehu ya ce daga cikin mutanen sun hada da mata bakwai yara biyu da kuma maza shida.
Kakakin ya ce ‘yan bindigan sun yi garkuwa da mutanen ne a ranar Talata.
Kazalika Shehu ya bayyana cewa bayan ceto mutanen an duba lafiyar su daga bisani kuma za a mika su ga ‘yan uwansu.