Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta tabbatar da kama kunshin kwayoyi masu yawa a wasu Jihohi hudu da ke Najeriya.

Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta ce ta kama tabar wiwi mai nauyin kilo 3,975kgs da kuma kwayar tramodal 58,200.

Hukumar ta bayyana cewa ta kama kwayoyin ne a yayin wani binciken da ta gudanar a garin Kano Kaduna Legas da kuma Imo.

Sanarwar ta kara da cewa a yayin simame ta kama mutane 11 da su ke da hannu a cikin kwayoyin.

Sanarwar ta kuma bayyana yadda mutanen su ke boye kwayoyin su shigo da ita Najeriya harma su fita da ita kasashen ketare.

Leave a Reply

%d bloggers like this: