Mahara da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace tsohon dan Majalisar Dokokin Jihar Edo, Fessu Edughele.

Rahotanni sun ce maharan sun yi awon gaba da Honorebul Ubiaja ne a safiyar Litinin, a hanyarsa ta zuwa Benin, babban birnin jihar daga Karamar Hukumar  Esan ta Arewa maso Gabas ta jihar.

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Edo, Festus Ebea, ya ce, an sace Honorebul Ubiaja ne a yankin Ubiaja da ke hanyar Orhionmwon zuwa Benin.

Ya so ya bi jirgin kasa zuwa Ubeaja, amma hakan bai yiwu ba saboda an dakatar da aikin jirgin Ubeaja zuwa Abuja.

Yan bindiga sun sace tsohon dan majalisar ne kwana uku bayan mahara sun yi garkuwa da fasinjoji 32 a tashar jirgin kasa ta Ebeaju da ke jihar zuwa Warri a Jihar Delta.

Festus Ebea ya ce, Iyalansa sun san an yi garkuwa da shi, an sanar da babban ofishin ’yan sandan yankin, suna fata za su kubutar da shi.

An nemi ji daga bakin kakakin ’yan sandan Jihar Edo, SP Chidi Nwanbuzor, domin karin bayani, amma har aka kammala hada wannan rahoton bai amsa kiran ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: