Masu garkuwa da mutanen da suka dauke Bayin Allah a tashar jirgin kas ana Ekehen a garin Igueben da ke jihar Edo, sun nemi a biya kudin fansa.

Rahoton da Daily Trust ta tattaro a ranar Litinin, ya nuna ‘yan bindigan sun tuntubi ‘yanuwan wadanda suka dauke, su na bukatar kowa ya biya N20m.


Wani jagoran matasa a yankin da abin ya faru, Benson Ordia ya tabbatar da lamarin, ya kuma bayyana cewa gwamnati tayi alkawarin kubutar da mutanen.
Shi kuwa SP Chidi Nwanbuzor wanda shi ne Mai magana da yawun ‘yan sanda na reshen jihar Edo, ya ce bai san da maganar neman kudin fansar ba.
A rahoton da aka samu, an tabbatar da cewa ‘yan ta’addan su na neman N20m daga hannun ‘yanuwan kowani mutum.
Wani mazaunin garin ya ce ya samu labari ne a wajen jami’an tsaro. ‘Yan sanda sun yi alkawarin za suyi bincike domin su gano gaskiyar wannan magana.